Embaló ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa zai dawo ƙasar domin shiga takarar shugabancin, duk da cewa bai bayyana takamaiman ranar dawowarsa ba a lokacin hirar. Sai dai daga baya ya sanar a shafukan sada zumunta cewa zai dawo Guinea-Bissau a ranar 4 ga Oktoba, yana mai kira ga al’umma da su tabbatar da zaman lafiya da jituwa.
Sojojin Guinea-Bissau sun karɓi mulki ne a ranar 26 ga Nuwamba, 2025, kwana guda kafin sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na wancan lokaci. Juyin mulkin ya kawo ƙarshen mulkin Embaló tare da dakatar da aikin zaɓen, wanda hakan ya janyo suka daga wasu masu sa ido kan harkokin siyasar ƙasar.
A halin yanzu, gwamnatin riƙon ƙwarya ƙarƙashin jagorancin Janar Horta N’Tam ce ke tafiyar da al’amuran ƙasar, bayan ta ayyana ranar 6 ga Disamba a matsayin ranar gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisa, da nufin mayar da mulki hannun farar hula. A ƙarƙashin dokar riƙon ƙwaryar, Janar N’Tam ba shi da damar tsayawa takarar shugaban ƙasa.
Duk da shirin dawowar Embaló, yanayin siyasar Guinea-Bissau na ci gaba da kasancewa cikin tashin hankali, yayin da wasu ’yan adawa ke kira ga jama’a da su kaurace wa zaɓen. Ƙasar dai ta sha fama da juyin mulki da yunƙurin kifar da gwamnatoci tun bayan samun ’yancin kai daga Portugal a shekarar 1974.
