Saurari premier Radio
22.1 C
Kano
Tuesday, September 24, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiTsohon firaministan Jamhuriyar Nijar Hama Amadou da ke adawa da hambararren shugaba...

Tsohon firaministan Jamhuriyar Nijar Hama Amadou da ke adawa da hambararren shugaba kasa Mohamed Bazoum ya koma Yamai bayan shafe fiye da shekaru biyu yana zaman jinya a kasar Faransa.

Date:

Tsohon firaministan Jamhuriyar Nijar Hama Amadou da ke adawa da hambararren shugaba kasa Mohamed Bazoum ya koma Yamai bayan shafe fiye da shekaru biyu yana zaman jinya a kasar Faransa.
Hama Amadou ya shafe shekaru biyu a Faransa yana jinya kafin ya koma Nijar.
Danginsa da sauran mukarrabansa sun yi amfani da shafukan sada zumunta wajen sanar da dawowarsa Nijar.
Dama dai bayan juyin mulkin 26 ga watan Yuli, Hama Amadou ya bayyana aniyarsa ta komawa, domin bada gudunmawa a babban taron kasa da jagoran mulkin soja Janar Adbourahamane Tiani ya yi alkawarin shiryawa.
Shi dai Hama Amadou da ya taba zama kakakin majalisar dokoki ya kasance a tsare a gidan yari, bisa zargin haddasa tashe-tashen hankula bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasa da Mohamed Bazoum ya lashe.
Duk da hasashen da aka dade ana yi cewa zai taka rawa a zaben shugaban kasa na 2021, amma Hama Amadou bai samu damar tsayawa takara ba saboda hukuncin daurin shekara daya a gidan yari a shari’ar fataucin jarirai, wanda ya bayyana a matsayin “makirci” da aka kulla da nufin hana shi zawarcin kujerar mulkin kasarsa.
Hama Amadou da ya kafa jam’iyyar Lumana ya taba zama firaministan Nijar sau biyu, na farko karkashin shugabancin Mahamane Ousmane da kuma karkashin mulkin marigayi Mamadou Tandja.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...