Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar sanya ƙarin harajin kashi 100 kan Kanada idan ta kuskura ta ƙulla yarjejeniyar kasuwanci da China.
Ya yi gargaɗin cewar China za ta haɗiye Kanada, ta hanyar amfani da ƙasar wajen sayar da kayyakin da ta yi niyyar shigarwa Amurka.
Dangantaka tsakanin Amurka da Kanada ta yi tsami tun bayan da Mista Trump ya koma mulki a karo na biyu, amma rashin jituwar ta tsananta a baya-bayan nan.
Mista Trump ya janye gayyatar da ya yi wa Mista Carney na shiga ”Kwamitin zaman lafiyar Gaza” bayan da firaministan na Kanada ya soki wasu manufofin gwamnatin Trump.
