Jami’an hukumar tsaro ta Civil Defence reshen Jihar Kano sun dakile wani yunkurin satar mutane da kuma satar shanu a garin Bakin Komau da ke Dangora, a karamar hukumar Kiru a nan Kano.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar SC Ibrahim Abdullahi, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a.
Sanarwar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis lokacin da wasu dauke da makamai suka kai hari kan wani makiyayi, inda suka jikkata shi tare da yin garkuwa da ‘ya’yansa biyu yayin da suke kokarin sace dabbobinsa.
Ibrahim Idris Abdullahi ya ce an ceto mutanen biyu da aka sace, da suka hada da Abubakar Saleh mai shekaru 36 da Muhammad Inuwa Dille mai shekaru 30, makiyayin da aka jikkata, Alhaji Saleh mai shekaru 70, ya samu kulawar lafiya cikin gaggawa.
Kwamandan hukumar ta Civil Defence a nan Kano, Mohammed Hassan Agalama, ya tabbatar wa mazauna jihar nan cewa hukumar za ta ci gaba da kare rayuka, dukiyoyin al’umm.
Hukumar ta kuma bukaci jama’a su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen dakile barazanar tsaro cikin gaggawa
