Saurari premier Radio
25.8 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiTinubu ya nada hakimin Dambatta a matsayin shugaban hukumar gudanarwar bankin masana’antu...

Tinubu ya nada hakimin Dambatta a matsayin shugaban hukumar gudanarwar bankin masana’antu na kasa

Date:

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Dakta Mansur Mukhatar a matsayin sabon shugaban hukumar gudanarwar bankin masana’antu na kasa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar a Litinin din nan, ta ce shugaban ya amince da nadin Dakta Mansur da karin mutane 12.

Dakta Mansur Muhtar wanda shi ne Sarkin Ban Kano, kuma Hakimin Dambatta ya zama sabon shugaban hukumar gudanarwar ne bayan amincewar shugaba Bola Tinubu.

A baya ya rike mukamin ministan kudi da kasafi daga shekarun 2008 zuwa 2010, kuma shi ne mataimakin shugaban bankin ci gaban musulunci.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...