Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabbin Kwamishinonin Zaɓe na Ƙasa guda uku domin cike guraben da ke akwai a Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, inda ya ce naɗin nasu zai fara aiki ne bayan Majalisar Dattawa ta tantance su tare da amincewa da naɗin.
Sabbin waɗanda aka naɗa sun haɗa da Farfesa Mustapha Aliu, wanda zai maye gurbin Farfesa Abdullahi Zuru a matsayin wakilin yankin Arewa maso Yamma.
Sauran sun haɗa da Bashir Muhammed Umar, wanda zai maye gurbin Farfesa Muhammad Adamu a matsayin wakilin yankin Arewa ta Tsakiya.
Haka kuma, Shugaba Tinubu ya zaɓi Oluwatoyin Babalola, wadda a yanzu take matsayin Kwamishiniyar Zaɓe ta Jihar Osun, domin wakiltar yankin Kudu maso Yamma a hukumar.
Babalola za ta maye gurbin Farfesa Cornelius Ajayi, wanda wa’adinsa zai ƙare a ranar 24 ga Oktoba, 2026.
Shugaba Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa da ta gaggauta tantancewa tare da amincewa da waɗanda aka naɗa, bisa la’akari da shirye-shiryen zaɓukan gama-gari da ake shirin gudanarwa a watan Janairu mai zuwa.
