Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiTINUBU, YA AMINCEWA KAMFANIN MAI NA KASA DA YAYI AMFANI DA RIBAR...

TINUBU, YA AMINCEWA KAMFANIN MAI NA KASA DA YAYI AMFANI DA RIBAR DA YA SAMU A 2023 DOMIN BIYAN TALLAFIN MAN FETUR.

Date:

Shugaba Bola Tinubu, ya amince wa Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), da ya yi amfani da ribar shekarar 2023 da aka samu domin biyan tallafin man fetur.

Daily trust ta rawaito jaridar the Cable, na cewa shugaban ya kuma amince da dakatar da biyan ribar da aka samu a 2024 ga gwamnati don taimakawa da kuÉ—aÉ—en da kamfanin zai kashe.

Ko da yake Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur din a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, sai dai akwai alamun da ke nuna cewar har yanzu gwamnati na kashe kuÉ—aÉ—e masu yawa a kan tallafin, duk da gwamnatin ta sha musanta biyan tallafin.

A baya-bayan nan dai ‘yan Najeriya suka yi zanga-zanga saboda wahalar da ake ciki a ƙasar nan, kuma ɗaya daga cikin buƙatun ‘yan kasar shi ne a dawo da tallafin man fetur din.

Amma a cikin wani jawabin da Tinubu ya yi, ya bayyana cewa dawo da tallafin man fetur ba zai yiwu ba, inda ya bayyana cire tallafin a matsayin abu mai wahala amma kuma wajibi ne gwamnatinsa ta yi.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...