Wata kotu a Ghana ta yankewa ɗaya daga cikin fitattun ƴan adawar ƙasar hukuncin daurin shekara 20 a gidan yari bayan samunsa da laifin haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.
Kotun ta samu Bernard Antwi Boasiako, shugaban jam’iyyar New Patriotic Party (NPP) da laifuka shida, ciki har da ba da umarnin gudanar da haƙar zinari ba tare da bin ƙa’ida ba.
An ce wannan ne mafi tsaurin hukunci da aka taɓa yanke wa wani babban ɗansiyasa a Ghana kan laifukan da suka shafi haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.
Wannan lamarin a cewar hukumomin ƙasar ya daɗe yana haifar da matsalolin gurɓata muhalli da lalata albarkatun ƙasar.
