Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya yaba wa dakarun sojin kasar nan,sakamakon daƙile wani yunkurin harin ’yan bindiga a Sabon Birni dake jihar.
Mai bai wa gwamna shawara kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya), ne ya bayyana hakan, inda ya ce ’yan bindigar sun yi yunƙurin kai wa ’yan kasuwa hari yayin da suke tafiya daga ƙauyen Tarah don cin kasuwar mako-mako, amma sojoji suka daƙile harin.
Saukar jirginmu a Burkina Faso ba laifi bane – Sojojin Saman Najeriya
Ƴan sandan Sokoto sun kama mutane 3 da ake zargi da daukar nauyin ƴan ta’adda
Usman, ya ce sojojin sun yi saurin ɗaukar mataki, wanda ya hana afkuwar mummunan hari.
Ya gode wa rundunar sojoji saboda jajircewarsu, tare da kira gare su da su ci gaba da kawar da ’yan ta’adda a Sakkwato da Arewa maso Yamma.
Gwamnan ya kuma roƙi jama’a da su riƙa ba da sahihin bayanai ga jami’an tsaro, sannan ya gargaɗin duk wanda aka kama yana taimaka wa ’yan bindiga zai fuskanci hukunci.
Ya ƙara da cewa Gwamna Ahmed Aliyu zai ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da duk abin da suke buƙata.
