Saurari premier Radio
25.8 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin Kano ta bai wa masu kasa kaya akan hanyar BUK wa’adin...

Gwamnatin Kano ta bai wa masu kasa kaya akan hanyar BUK wa’adin kwana guda su tashi

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta umarci wadanda suka ajiye kayan kasuwancin su ba bisa kai’ida ba akan hanyar sabuwar jami’ar Bayero zuwa Tal’udu su gaggauta cire su nan da awanni ashirin da hudu.

Daraktan mulki da gudunarwar na ma’aikatar kasa da tsare-tsare, Hamid Sidi Ali ne ya bayyana haka jim kadan bayan da ya jagoranci kwamitin da gwamnatin Kano ta kafa domin tsaftace gine-ginan da aka yi ba bisa kai’ida ba.

Ya ce da yawa daga cikin wuraren da kwamitin ya sanya wa alamar jan fenti ana gudanar da kasuwancin ne akan magundanan ruwa wanda kuma hakan barazana ce musamman a wannan lokaci na damuna.

Daraktan ya kuma bukaci wadanda suke gine-ginan ba bisa kai’ida ba da su cire su kafin karewar wa’adin da kwamitin ya basu.

Wakilinmu Ibrahim Aminu Riminkebe, ya rawaito cewa kwamitin ya yi alkawarin daukar matakin doka kan duk wanda ya bijirewa umarnin da aka bashi.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...