Ɗan majalisar da ke wakiltar Tudun Wada, Sule Lawan Shuwaki, ne ya gabatar da ƙudirin gaggawa a zauren majalisar, inda ya bayyana cewa ambaliyar ta faru ne a ranar Alhamis da ta gabata, ta kuma janyo asarar amfanin gona da dama ga manoman yankin suka shafe watanni suna nomawa.
Ya kuma bayyana cewa ruwan sama ya lalata wata tsohuwar gada da ke kan hanyar Tudun Wada zuwa Shuwaki, lamarin da ya kawo cikas ga zirga-zirgar jama’a, musamman ɗalibai da sauran mazauna yankin, hakan ya shafi harkokin tattalin arziki da zamantakewar al’umma, tare da ƙara wa manoma wahalar isa gonakinsu.
Sule Lawan Shuwaki ya roƙi gwamnatin jihar da ta samar da kayan agaji da sauran tallafi ga manoman da abin ya shafa, tare da gaggauta gyara gadar da hanyar domin rage wa mazauna yankin wahalhalun da suke fuskanta, ɗan majalisa mai wakiltar Gezawa, Abdullahi Yahaya Tsamiyar Kara, ne ya mara wa ƙudirin baya.
Bayan muhawara, majalisar ta amince da ƙudirin tare da kira ga gwamnatin jihar da ta ɗauki matakin gaggawa kan lamarin, wannan mataki na zuwa ne yayin da manoma ke fuskantar ƙalubalen asarar amfanin gona sakamakon ambaliyar ruwa, lamarin da ka iya shafar samar da abinci da tattalin arziƙin al’ummomin da abin ya shafa.
