Rundunar Operation Hadin Kai ta bayyana sunayen wasu manyan shugabannin ƙungiyar ISWAP da hukumomin tsaro ke nema ruwa a jallo.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar, ya ce wanda aka fi kowanne nema shi ne Abu Musa Al-Mangawi Baa Shuwa, wanda aka bayyana a matsayin shugaban ISWAP a yankin Tafkin Chadi.
Sauran da aka ambata sun haɗa da mataimakinsa, Muhammad Jidda da kuma Hamad Abu Hanifa, wanda ake kira Amirul-Fiya na ƙungiyar ISWAP.
Rundunar ta ce ta gano waɗannan bayanai ne bayan da sojoji suka ƙwato wasu muhimman kayayyakin fasaha daga yan ta’adda, ciki har da kyamarar bidiyo da ake amfani da ita wajen ɗaukar faifan farfaganda da kuma rikodin ayyukan ƙungiyar.
Binciken da aka gudanar kan waɗannan na’urori ya taimaka wajen gano sansanonin yan ta’addan da kuma tantance wasu daga cikin manyan shugabanninsu da ke aiki a ƙananan hukumomin Abadam da Kukawa na Jihar Borno.
Rundunar ta kuma sanar da cewa za ta ba da lada mai tsoka na Naira miliyan 60 ga duk wanda ya bayar da sahihan bayanai da za su kai ga kama waɗannan mutanen da ake nema.
Sai dai ta yi gargaɗi ga jama’a da kada su yi yunƙurin kama ko tunkarar waɗanda ake zargin, tana mai roƙon su riƙa isar da duk wani sahihin bayani ga hukumomin tsaro ta hanyoyin da aka tanada ko kuma ta lambar waya 07084988859.
Rundunar ta jaddada cewa za a kiyaye sirrin duk wanda ya bayar da bayanai domin tabbatar da tsaronsa.
