Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Esther, ta amince cewa ofishinta ya yi kuskure wajen bayar da amincewar ɗaukar ma’aikata ga hukumar PFIPC, wadda ake zargin hukuma ce ta bogi, ba tare da gudanar da cikakken bincike ba.
Walson-Jack ta ce amincewar da ofishinta ya bayar ta dogara ne da bayanan da aka gabatar mata a lokacin, tana mai jaddada cewa babu wata manufa ta kauce wa ƙa’idoji ko karya doka.
Ta kuma tabbatar da cewa ofishinta na ba da cikakken haɗin kai ga binciken da ake gudanarwa domin gano yadda lamarin ya faru.
Ana zargin Prince Adeniyi Adeyemi Mathew da gudanar da Hukumar PFIPC ba tare da sahalewar gwamnatin tarayya ba, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce bayan an gano cewa an ware wa hukumar kuɗi a cikin kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2026.
A halin yanzu, Kwamitin Majalisar Wakilai mai kula da lamarin na ci gaba da gudanar da bincike domin gano waɗanda suka taka rawa a lamarin.
