Saurari premier Radio
33.3 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiShugaban kasa Bola Ahmad Tinubu yayi wa Abdullahi Ganduje tayin Ambasada.

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu yayi wa Abdullahi Ganduje tayin Ambasada.

Date:

Wasu rahotanni na cewa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya yiwa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, tayin mukamin ambasada a daya daga cikin kasashen Afrika.

Jaridar Daily Nigerian da ta wallafa labarin ta ce wasu majiyoyi sun tabbatar mata da cewa, Tinubu ya wakilta shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, domin ya sanar wa da Ganduje wannan tayi.

Majiyoyin sun ce Akpabio ya sanar da Ganduje cewa, Tinubu na son ba shi mukamin jakadan ne domin Gandujen ya kaucewa zarge-zarge cin hanci da rashawa da ake masa a nan Kano.

Sai dai jaridar ta Daily Nigerian ta ce Ganduje ya yi watsi da tayin da Tinubun ya yi masa, ya na mai bayyana zarge-zargen a matsayin na karya kuma zai yi nasara a kotu.

Haka kuma wasu rahotannin sun ce shugaban kasar da kansa ya sanar da Ganduje tayin bashi mukamin na ambasada tare da bashi damar zabar duk kasar da yake so a tura shi a nahiyar Afrika, yayin da wasu majiyoyin suka ce an bashi damar zabar kasa a nahiyoyi uku na afrika, Asia da Europe.

 

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...