Saurari premier Radio
22.6 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiShugaban kamfanin Novomed dan uwa ga Sanata Rabiu Kwankwaso ya ƙalubalanci binciken...

Shugaban kamfanin Novomed dan uwa ga Sanata Rabiu Kwankwaso ya ƙalubalanci binciken da hukumar yaƙi da rashawa keyi masa.

Date:

Shugaban kanfanin saida maganguna na NOVOMED, Musa Rabiu Kwankwaso, daya kasance  ɗan uwa ga sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ƙalubalanci binciken da wasu hukumomin yaƙi da rashawa uku suke gudanarwa a kansa kan zargi ɗaya kuma a lokaci guda.

Musa Kwankwaso wanda yake tare da tawagar lauyoyinsa ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan ya amsa gayyatar da Hukumar Karɓar Korafe-Korafe da Yaƙi da Rashawa ta Jihar Kano tayi masa a  Alhamis din nan.

A bayan nan dai ana ta cece-kuce kan wata kwangila wadda ta shafi kai wa ƙananan hukumomin Jihar  nan 44 magunguna.

Cece-kucen na zuwa ne bayan ɓullar wani bidiyo da mai barkwanci nan a dandalan sada zumunta, Bello Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello ya fitar, inda yake zargin Gwamnatin Kano da bai wa wani kamfani na Novomed kwangilar siyan magunguna.

A bidiyon, Dan Bello ya yi zargin gwamnatin Kano da bai wa ɗan uwan tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso kwangilar siyan magungunan inda ya ce a duk wata kowace ƙaramar hukuma ta Kano na bayar da naira miliyan tara ga kamfanin na Novomed mallakar Musa Garba Kwankwaso.

Sai dai kuma Fitar bidiyon ke da wuya, Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya ce ba shi da masaniya kan lamarin, ya bayar da umarni ga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar kan ta gudanar da bincike nan take sannan ta gabatar da rahoto game da hakan domin ɗaukar mataki.

A cewar hukumar karbar koarafe korafe da yaki da cin hanci da rasahawa ta nan Kano, kawo yanzu an gano naira miliyan 160 daga cikin naira miliyan 440 da ake nema kan kwangilar da ba ta da asali a hukumance.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...