Saurari premier Radio
29.3 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiSenegal ta kafa kwamitin da zai bibiyi yarjejeniyar man fetur da iskar...

Senegal ta kafa kwamitin da zai bibiyi yarjejeniyar man fetur da iskar Gas.

Date:

Gwamnatin Senegal ta kafa wani kwamiti da zai yi aikin duba da kuma sake daidaita yarjejeniyar man fetur da iskar Gas da ƙasar ta ƙulla da ƙasashe ko kuma kamfanonin ƙetare.

Prime ministan ƙasar Ousmane Sonko ne ya bayyana hakan bayan shan alwashin daidaita tsarin fitar da man fetur na ƙasar da ya dauka.

Ƙasar ta yammacin Afrika ta shiga cikin jerin ƙasashe masu fitar da man fetur a watan Yulin da ya gabata kuma ta kammala duk wani shirye-shirye don fara fitar da iskar Gas a ƙarshen shekarar da muke ciki.

Tun bayan da aka rantsar da shi a watan Maris ɗin da ya gabata Shugaban ƙasar Bassirou Dimomaye Faye ya sha alwashin gudanar da bincike da kuma sanya idanu a fannin na man fetur da iskar Gas don hana duk wata almundahana shiga.

Sabuwar gwamnatin ta ce yarjejeniyoyin man fetur ɗin da tsohuwar gwamnati ta ƙulla da ƙasashe da kuma manyan kamfanonin duniya ba zai amfani ƙasar da komai ba.

A wajen taron ƙaddamar da kwamitin Sonko ya ce abin takaici ne yadda tsohuwar gwamnati ta shiga yarjejeniya bayan tana gani baro-baro cewa ka’idojin zasu cutar da ƙasar ne.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...