Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ziyarci Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima a gidan sa, domin taya shi murnar zaɓensa a matsayin mataimakin ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, a zaɓen shekarar 2027.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Gwamnan ya bayyana cewa zaɓen Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakin ɗan takarar wata alama ce ta amincewa da irin gudummawar da yake bayarwa wajen hidimtawa ƙasa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma roƙi Allah kan ya baiwa Shugaba Tinubu da Mataimakinsa hikima, lafiya da nasara yayin da suke shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa Gwamnan ya kuma sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da marawa duk wani ƙoƙari da ke ƙarfafa haɗin kan ƙasa, zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a Najeriya.
