Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya daga likkafar wasu hakimansa 14

0
281

Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu ya daga likkafar wasu daga cikin hakimansa guda goma sha hudu 14.

Sarkin ya daga darajar Alhaji Munnir Sunusi Bayero, daga Dan Buran din Kano zuwa Wamban Kano hakimin bichi Dan majalisar sarki, sai kuma Alhaji Kabiru Tijjani Hashim, Daga Dan Isan Kano zuwa Turakin Kano, Alhaji Mujittapha Abubakar Abba, Daga Falakin Kano zuwa Sarkin Yakin Kano, sai Alhaji Umar Sunusi Daga Bunun Kano zuwa Dan Buram din Kano, Ɗan Galadiman Alhaji Haruna Rasheed Bayero zuwa Ɗan Iyan kano, sai Alhaji Abdullahi Lamido Sunusi Turakin Kano zuwa Barden Kano, Alhaji Yahaya Inuwa Abbas Dan majen Kano zuwa Ɗan Galadiman Kano.

Akwai Alh. Umaru Sunusi bunun Kano zuwa Ɗan Buran, Alhaji Bashir Ado Bayero Dan lawan zuwa Ɗan Isa, Alhaji Bello Ado Bayero dan darman Kano zuwa Ɗan Lawan.

Karin girman ya haɗa da Ɗan Madami Alhaji Ibrahim Hamza Bayero zuwa Ɗan Majen kano, sai Yariman kano Alhaji Abdullahi Abubakar Bayero zuwa Ɗan Darman kano sai Zannan kano Alhaji Aminu Sadiq zuwa Bunun Kano sannan Fagacin Kano Alhaji Habib Bello Ɗan kadai zuwa katukan Kano, sai na 14 Ɗan malikin Kano Ambasada Ahmad Umar zuwa Jarman Kano.

Mai martaba sarkin ya bayyana dalilinsa na dagacin darajar hakiman ya kuma ja hankalinsu dasu gudanar da aikinsu cikin gaskiya da rikon Amana.

Wakilinmu na masarautar Kano Ammar Shanono ya rawaito cewa nadin sarautar ya sami halartar mataimakin Gwamnan jihar Kano kwamared Aminu Abdussalam da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El’rufa’i da sauran manyan baki daga ciki da wajen kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Captcha verification failed!
CAPTCHA user score failed. Please contact us!