Saurari premier Radio
22.5 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSanata Barau ya jagoranci bai wa yan jihar Kano 70 takardar samun...

Sanata Barau ya jagoranci bai wa yan jihar Kano 70 takardar samun gurbin karatu domin yin digiri na biyu a jami’oin kasashen waje

Date:

Mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibrin ya jagoranci bai wa yan jihar Kano 70 takardar samun gurbin karatu domin yin digiri na biyu a jami’oin kasashen waje.

Bikin bayar da takardun samun gurbin karatun ya gudana a nan Kano, da akalla daliban 70 su ka amfana da karo karatun digiri na biyu a fannonin fasahar sadarwa a jami’oi daban-daban na kasashen duniya.

Sanata Barau ya bayyana tsarin a amatsayin wanda zai taimaki ci gaban kasa, musamman yadda ake da karancin masu karatun bangaren fasahar sadarwa.

Ya kuma ce duka dalibai 70 din da suka amfana da tallafin karatun, an zabo sune bisa can-canta ba wai nuna bangarenci na siyasa ba.

Taron dai ya samu halartar karamin ministan ilimi, Dakta Yusuf Tanko Sununu da shugaban asusun bayar da lamunin karatu NELFUND, Jim Ovia da kuma tsohon shugaban jami’ar Bayero ta Kano FarfesaYahuza Bello.
AHG

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...