
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya bayyana salon siyasar kwakwaso na jajircewa wajen hidimar jama’a da ilimi da ci kuma gaban ƙasa na ci gaba da zama abin koyi ga al’umma daga ƙarni zuwa ƙarni.
Atiku ya bayyana hakan ne a wani saƙon taya murna da ya aike ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayin da yake cika shekaru 69 a duniya.
Atiku ya wallafa a sakonne a shafinsa na Facebook a ranar Litinin.
“Irin gudunmawar da Sanatan ke bayarwa wajen inganta rayuwar talakawa da gina ƙasa abin yabo ne”. In ji shi.
Atiku ya kuma ta ya Kwankwaso da iyalansa da abokansa da kuma magoya bayansa murna a wannan rana ta musamman
Ya kuma yi masa fatan alheri da ƙarin lafiya da ɗorewar nasara a rayuwarsa da ayyukansa na gaba.