Shugaba Tinubu ya taya ‘yan Najeriya murnar sabuwar shekara tare da fatan alheri da samarwa da kasar nan makoma mai kyau.
Shugaban ya kuma ƙarfafawa ’yan Najeriya gwiwa da su ci gaba da kasancewa masu haɗin kai.
Hakan na kunshe ne a cikin saƙon sabuwar shekarar da shugaban ya aike wa ‘yan kasar a ranar Laraba.
Tinubu ya tabbatarwa al’ummar kasar cewa, sadaukarwarsu na watanni 19 da suka gabata na mulkinsa ba za su tafi a banza ba.
“Al’umma sun fuskanci matsaloli a bara, amma ina mai baku tabbacin cewa sabuwar shekarar nan za ta kawo sauye-sauye masu kyau”.in ji shugaban.
Sannan ya kuma yi hasashen raguwar farashin man fetur da kara karfin asusun kasar na kasashen waje da habakar ciniki da kuma zuba jari.
Duk da haka shugaban ya yarda da cewa, hauhawar farashin abinci da sauran kayayyakin more rayuwa na ci gaba da zama babbar matsala.
Shugaban ya kuma bayyana shirin kirkirar kamfanin kula da lamuni na kasa, da zai taimaka wajen ba ’yan kasuwa damar samun rance.
Sannan ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su mayar da hankali wajen haɗin kai da kuma aiki tare domin gina ƙasa mai albarka.