Gwamnatin jihar Kano ta ce nan gaba kadan zata biya duk ma’aikatan shara da suke binta bashi, tare da bayyana shirinta na samar da ababen hawa na musamman da zasu dinga aikin debe sharar da al’umma kan tara a unguwannin birnin Kano.
Sabon kwamishinan ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi Dakta Dahiru Muhammad Hashim ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kai ziyarar gani da ido zuwa hukumar kwashe shara ta jihar Kano REMASAB.
Kwamishinan yace zai yi duk mai yiwuwa domin ganin ma’aikatan shara dake bin gwamnati hakkokinsu na albashi da alawaus sun samu hakkinsu, tare da fatan hakan zai taimaka wajen su rubanya aikin da suke domin tabbatar da tsaftar muhallan jihar baki daya.
Da yake nawa jawabin tun da fari mataimakin manajan daraktan hukumar kwashe shara ta jihar Kano REMASB Alhaji Lamin Mukhtar ya yi wa kwamshinan karin bayani kan aikin kwashe shara da suke ci gaba da yi ba dare ba rana a fadin Kano, tare da yi masa bayani kan irin feshin maganin sauron da suke ci gaba da yi a wasu daga cikin unguwannin Kano.