Kyautar Dalar ta janyo cece-ku-ce a shafukan sada zumunta tare da matsin lamba ga mawakin na sanin nawa shugaban da aka sani da tsantsaini ya ba shi.
Tsohon shugaban kasa Muhamadu Buhari yayi kyautar Dala Amurka ga wani mawaki a jihar Katsina.
Shugban ya yi wannan kyauta ta bazata ga mawakin ne a wani taron Jam’iyyar APC a jihar a farko makon jiya.
A wani hoton bidiyo ya karade shafukan sada zumunta an ga tsohon shugaban shi da wasu manyan shugabannin jam’iyyar da kuma gwamnan jihar a tsaye sun sauraron mawaki Dan Soja yana waka.
Cikin farin da anashuwa da kuma yabawa Buhari ya sa hannu a aljihu ya damko wasu ‘yan daloli ya mikawa mawakin, wanda hakan ya haifar da tafi da sowa daga jama’ar wurin.
A wata hira da mawakin ta wayar tarho, ya yi murna da kuma alfahari da wannnan kyauta ta tsohon shugaban kasar da mutane da yawa suka yiwa tambari da cewar kyautarsa ba ta wuce na shan ruwa.
“Ba dala dari ba ya bani ba, Daloli ne baba ya bani. Ba sai na fadi ko guda nawa ne ba… kuma abin ya shiga tarihi domin haka bai fi sa’oi ukiu ba aka yi ta kirana daga ko ina ta waya ta hara daga Jamani ana tambaya ta nawa ce. Wannan abin a yaba ne. Inji mawakin.
Daya daga cikin abin da tsohon shugaban na Najeriya ya yi fice da shi a zamanin mulkinsa shine tsantsaini da kuma alkinta abin hannu.
Don haka wannan kyauta da yayi ta dauki hankalin jama’ar kasar.