Jami’iyyar APGA ta kayar da APC a zaben jihar Anambra.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da Farfesa Chukwuma Charles Soludo na jam’iyyar APGA a matsayin wanda ya sake lashe zaɓen gwamna da aka gudanar a jihar Anambra ranar Asabar.
Soludo, wanda ya nemi wa’adi na biyu, ya yi takara ne tare da sauran ‘yan takara 15 da suka haɗa da Prince Nicholas Ukachukwu na APC, Paul Chukwuma na YPP, John Nwosu na ADC da George Moghalu na LP, da sauran su.
Da yake bayyana sakamakon ƙarshe, jami’in tattara sakamakon jihar, Farfesa Edoba B. Omoregie (SAN) ya bayyana cewa:
Jimillar masu kada kuri’a a jihar: 2,788,864
Adadin da suka fita aka tantance: 598,229
Kuri’un da suka inganta: 584,054
Kuri’un da aka ƙi karɓa: 11,244
Jimillar kuri’un da aka kada: 595,298
A sakamakon ƙuri’un da ‘yan takara suka samu:
APGA (Soludo): 422,664
APC (Ukachukwu): 99,445
YPP (Paul Chukwuma): 37,753
LP (Moghalu): 10,576
ADC (Nwosu): 8,208
Labarai masu alaka
Rahoton Masu sa ido
Masu Sa-ido na Cikin Gida da Na Waje Sun Koka Kan Sayen Kuri’u da Karancin Fitowar Masu Kada Kuri’a a Zaben Anambra
Masu sa-ido na kasa da kasa da na cikin gida sun bayyana damuwa kan yawaitar sayan kuri’u da kuma karancin fitowar masu kada kuri’a* a zaben gwamna da aka gudanar a ranar 8 ga Nuwamba a jihar Anambra.
Cikin rahoton da YIAGA Africa, hadin gwiwa da EU-SDGN II da sauran abokan hulɗa suka fitar, sun nuna cewa yawancin runfunan zabe a ƙananan hukumomi 21 na jihar sun fuskanci ƙarancin masu kada kuri’a.
Samson Itodo, Daraktan YIAGA Africa, ya bayyana cewa sayan kuri’u da ƙarancin fitowar jama’a na daga cikin manyan matsaloli da aka fi fuskanta.
Asabe Ndahi daga Kukah Centre ta nuna damuwa kan gurbacewar tsaro da jinkirin isowar jami’an INEC da na tsaro, musamman a wurare masu hadari irin su Nkwelle-Ezunaka, Ihiala, Ogbaru da Nnewi South. Ta kuma ce an samu rahoton sayan kuri’u da tsoratar da masu kada kuri’a a wasu kananan hukumomi.
Haka zalika, CDD-West Africa ta bayyana irin wannan damuwa.
Duk da haka, YIAGA ta ce rahotannin daga wakilanta a rumfunan zabe 250 sun nuna cewa kashi 85 cikin 100 sun fara tantancewa da kada kuri’a da wuri, yayin da kashi 86 cikin 100 suka samu na’urar BVAS.
