Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta kasa NCDC ta ce an gwada mutanen da ake zargin sun kamu da Ebola a Adamawa, kuma sakamakon ya nuna ba su da cutar.
NCDC, ta ce mutanen biyu da aka killace a birnin Yola, ba su da cutar Ebola bayan gudanar da gwaje-gwaje sau biyu.
Babban Daraktan NCDC, Dokta Jide Idris, ya ce babu wani tabbataccen mai ɗauke da cutar Ebola a jihar Adamawa a halin yanzu.
Ya ƙara da cewa, matar da aka tabbatar ya kamu da cutar a babban birnin tarayya Abuja, shi ne kaɗai aka tabbatar ya kamu da cutar a Najeriya, wadda tuni aka fice da ita zuwa Switzerland.
NCDC ta ce tana haɗin gwiwa da gwamnatin jihar Adamawa da sauran hukumomin lafiya domin sa ido kan lamarin da kuma ɗaukar matakan kariya.
Hukumar ta shawarci duk wanda ya fara fama da zazzaɓi, matsananciyar kasala, ciwon kai, ciwon jiki, amai ko gudawa, musamman idan ya yi mu’amala da wanda ake zargin yana ɗauke da cutar, da ya garzaya asibiti.
