Saurari premier Radio
24.8 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiJAGORORIN DARIKAR SHI’A SUN MUSANTA ZARGIN DA RUNDUNAR YAN SANDA TAYI NA...

JAGORORIN DARIKAR SHI’A SUN MUSANTA ZARGIN DA RUNDUNAR YAN SANDA TAYI NA CEWA SUN FARMAKI JAMI’ANTA

Date:

Jami’an ’Yan Sanda biyu sun rasa rayukansu yayin da wata arangama da ta ɓarke tsakaninsu da mabiya ɗariƙar Shi’a (IMN), a kasuwar Wuse da ke Abuja.

Kazalika, an harbe wani ɗan kasuwa mai suna Amiru, yayin da yake ƙoƙarin tserewa lokacin ta tarzomar ta tashi, inda daga bisani ya rasu a hanyar zuwa asibiti.

Rikicin dai ya fara ne lokacin da ’yan Shi’a da ke gudanar da tattaki suka yi arangama da ’yan sanda.

Sun yi wa jami’an ƙawanya, inda suka ƙwace makamansu, sannan suka ƙone motocin ’yan sanda uku.

A martanin da rundunar ’yan sandan Abuja, ta mayar kan lamarin, ta bayyana harin a matsayin abun takaici.

Amma rundunar ta tabbatar da cewa an kama mutane da dama da ke da alaƙa da rikicin.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yansandan babban birnin SP Josephine Adeh, ta fitar, ta tabbatar da kisan jami’ansu guda biyu da jikkata wasu biyu tare kuma da kona motocin ‘yansanda na sintiri uku a rikicin wanda ta ce ba gaira ba dalili mabiya kungiyar suka kai wa jami’ansu hari.

Kwamishinan ’yan sandan Babban Birnin Tarayya, CP Benneth C. Igweh, ya yi Allah-wadai da tashin hankalin.

Ya kuma lashi takobin gurfanar da waɗanda suka aikata laifin a gaban kuliya.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...