Saurari premier Radio
25.2 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiTsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya kudiri aniyar haɗa kan arewa...

Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya kudiri aniyar haɗa kan arewa da samar da yankin mafitar siyasa.

Date:

Wata sabuwar ƙungiya ta wasu gogaggun ‘yansiyasa a arewacin kasar nan, ta ce ta fara lissafin samar da mafita ga yankin.

Wasu da suka kira kansu masu kishin arewacin Najeriya sun ɓullo da sabon yunƙurin ne da nufin sama wa yankin ingantaccen shugabanci da alkibla ta fuskar siyasa da tattalin arziki da zamantakewa.

Sun kira wannan yunƙuri nasu da taken ”League of Northern Democrats”, a turance – wani taron dangi na wasu masu fada a ji na areawacin Najeriya, da suka hada da tsofaffin gwamnoni da ma’aikatan gwamnati da ‘yansiyasa da tsofaffin sojoji da ‘yan sanda, da sauran masu ruwa da tsaki na yankin.

Taron da suka gudanar a Abuja ranar Talata, ya amince da naɗa tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan Ilimi Malam Ibrahim Shekarau a matsayin jagora.

Mahalarta taron sun ce sun yi la’akari da zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a ƙasar wadda ta ƙara nuna wa duniya irin girman ƙalubalen da yankin arewa ke fuskanta.

Sun ce ɗaya daga cikin babbar manufarsu ita ce haɗa kan al’ummar arewa da samar wa yankin mafitar siyasa.

A cewar ƙungiyar, hadin kan arewa ne zai zama ginshiƙin farfaɗo da arewa a matsayin jagaba a fagen siyasar Najeriya.

Yankin arewacin Najeriya dai na fuskantar tabarbarewar al’amura da koma-baya a fannoni da dama na ci gaba, musamman tsaro da ilimi da tattalin arziki.

Amma wasu masu sharhi sun bayyana wannan yunƙurin na ƙoƙarin farfaɗo da yankin a matsayin wata manufar siyasa, kuma ƙungiyar na iya rikiɗewa ta koma wata jam’iyyar siyasa idan tafiya ta yi tafiya, musamman la’akari da rarrabuwan kan shugabannin yankin.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...