Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya yi wa fursunoni 130 afuwa, tare da sauya hukuncin kisa da aka yanke wa wasu fursunoni huɗu zuwa ɗaurin rai da rai, a wani mataki na bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya.
Gwamnan ya ɗauki matakin ne bayan shawarwari da Majalisar Ba da Shawarar Afuwa ta Jihar Plateau, bisa ikon da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi na yin afuwa ga waɗanda aka yanke wa hukunci.
Waɗanda aka sauya wa hukuncin kisa zuwa ɗaurin rai da rai sun haɗa da Zuhumnan Musa, Jeremiah Aese, Pam Lang da Thoma Danboyi.
A cikin saƙon taya ’yan Najeriya murnar zagayowar ranar ’yancin kai, Gwamna Mutfwang ya buƙaci al’umma da su yi tunani kan tafiyar ƙasar tun bayan samun ’yancin kai a shekarar 1960, tare da girmama sadaukarwar waɗanda suka kafa ta.
Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kai, zaman lafiya da kishin ƙasa, yana mai cewa gina ƙasa nauyi ne da ya rataya a wuyan kowane ɗan ƙasa, domin tabbatar da makoma mai kyau ga al’umma masu zuwa.
