
Aminu Abdullahi Ibrahim
An yi kunen doki da ci 1-1 a wasan kwallon kafa tsakanin ‘yan jaridar gidan gwamnati da ‘yan social media na jam’iyar NNPP.
An gudanar da wasan sada zumuncin ne a harabar filin wasa na gidan talabijin na ARTV dake Kano da yammacin ranar Talata.
An shirya wasan domin taya wakilin gidan rediyon Nasara, Jabir Ali Dan Abba murnar karuwar Da Namiji da ya samu.
Wasan ya kunshi ‘yan jarida wakilan kafafan yada labarai daban-daban dake aiki a gidan gwamnatin Kano da ‘yan social media.
Sadiq Iliyasu shine Kocin da ya jagoranci ‘yan jarida a wasan kwallon kafar, yayin da Nura Muhammad Dandago ya jagoranci bangaren ‘yan social media.
Bayan kammala wasan an karrama daraktan yada labarai na gidan gwamnati Usman Gwadabe da shugabar gidan talabijin ta ARTV Hauwa Isa Ibrahim.