Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya taya Sarkin Musulmi kuma shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na Uku, murnar cika shekaru 20 da hawa karagar mulkin masarautar Sokoto.
Gwamnan ya bayyana matsayin da cewa muhimmin lokaci ne, na jinjinawa gudunmawar da Sarkin Musulmin ya bayar wajen jagorancin addini, haɗin kan ƙasa, zaman lafiya da haɓaka fahimtar juna tsakanin al’ummar Najeriya.
Gwamna Abba ya yaba da rawar da Sarkin Musulmin ke takawa wajen yaɗa kyawawan koyarwar Musulunci, ƙarfafa dangantaka tsakanin mabiya addinai da samar da tattaunawa da fahimtar juna tsakanin al’ummomi masu bambancin addini da al’adu.
Haka kuma ya bayyana jagorancin Sarkin Musulmin a matsayin tushen ci gaba da kasancewa ginshikin shiriya ga al’ummar Musulmi, tare da taimakawa wajen ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a Najeriya.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Abba na rokon Allah ya ƙarawa Sarkin Musulmin lafiya, hikima da ƙarfin guiwa wajen ci gaba da hidimtawa Musulunci, al’ummar Musulmi da ƙasa baki ɗaya.
