Saurari premier Radio
22.6 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiGwamnatin tarayya ta bayyana shirin samar da jarin dalar Amurka biliyan 100...

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin samar da jarin dalar Amurka biliyan 100 domin samar da ayyuka a bangaren ƙere-ƙere da al’adu.

Date:

Ministar Al’adu da Ƙirƙira, Hannatu Musa Musawa, ta bayyana shirin samar da jarin dalar Amurka  biliyan 100 domin samar da ayyuka miliyan biyu a ɓangaren ƙere-ƙere da al’adu domin farfaɗo da tattalin arzikin Kasar nan.

Ministan na bayyana hakanne a wata hira da ta yi da manema labarai, inda ta ce suna da zummar cimma wannan muradi ne domin ganin an samu kaso mai tsoka a kasuwar duniya na sama da dala tiriliyan 1 a cikin Ma’aikatar Al’adu da Ƙirƙira ta Nijeriya wanda ya yi daidai da manufofin gwamnati mai ci.

Hannatu Musawa ta ce  hakan yana yiwuwa tare da damar shiga cikin ƙirƙirar al’adu da ƙimar tattalin arzikin al’adu ta hanyar manufofin ba da damar yanayin kasuwanci.

Ministar ta kuma sanar da kulla haɗin gwiwa da Gidauniyar BigWin, wata babbar abokiyar ci gaban ƙasa da ƙasa, don samar da ayyukan yi da dabarun masana’antu.

A cewar ministar, ma’aikatar ta mayar da hankali ne kan kulla haɗin gwiwa da gidauniyar BigWin la’akari da nasarar da ta samu wajen samar wa matasa ƙasar Rwanda 500,000 ƙwarewa a fasahar zamani domin dogaro da kai da kuma samar da ayyukan yi ga miliyoyi jama’a a ƙasar Cote d’Ivoire.

Musawa ta ci gaba da cewa ma’aikatar tana ƙoƙarin aiwatar da wasu muhimman ayyuka a sassa huɗu domin samar da ayyukan yi miliyan biyu a fannin ƙirƙire-ƙirƙire ta hanyar haɗin gwiwa da BigWin.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...