Saurari premier Radio
27.4 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAkwai yiyuwar fuskantar karin farashin man fetur a Najeriya

Akwai yiyuwar fuskantar karin farashin man fetur a Najeriya

Date:

Kamfanin mai na kasa NNPCL, ya ce masu shigo da fetur na bin dimbin bashin da ya ce yana barazana ga ɗorewar shigo da fetur ƙasar nan.

Kakakin kamfanin, Olufemi Soneye, ya ce ɗimbin bashin ya sanya matsi sosai, amma suna haɗa kai da hukumomin gwamnati da al’amarin ya shafa da sauran masu ruwa-da-tsaki domin ci gaba da raba fetur din a faɗin ƙasar nan.

Kamfanin ya fitar da sanarwar ne dai-dai lokacin da yan Nijeriya ke shafe sa’o’i da dama suna layi a gidajen mai ba tare da samun shi ba saboda ƙarancinsa.

Farashin lita ɗaya na fetur ya ninninka, tun bayan da shugaba Bola Tinubu ya janye tallafi a watan Mayun bara, al’amarin da al’ummar ƙasa ke ganin shi ya haddasa tashin gwauron-zabon da kusan kayayyaki suka yi.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...