Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris Kauran Gwandu ya bayyana cewa babu wani ɓangaren jihar da ke ƙarƙashin ikon ’yan bindiga.
Sanarwar ta fito ne daga Mai Bai wa Gwamnan Shawara kan Yaɗa Labarai, Yahaya Sarki, inda aka ce Gwamna Idris ya bayyana hakan ranar Litinin a yayin taron tattaunawa kan sha’anin tsaro da ƙungiyar masu harkokin yaɗa labarai suka gudanar a Birnin Kebbi.
“Duk da cewa gwamnatinsa ta gaji wasu matsalolin tsaro, an samu gagarumar nasara wajen magance su ta hanyar haɗin gwiwa da hukumomin tsaro, musamman wajen samar da kayan aiki da tallafin sufuri.
“’Yan bindiga na aiki ne a tsorace, suna kai hari su gudu, saboda suna shakkar irin shirin da jami’an tsaro ke da shi. In ji shi.
Gwamnan ya yaba wa shugabannin tsaro bisa jajircewarsu, sannan ya bayyana taron a matsayin dama ta musayar ra’ayoyi kan hanyoyin magance matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar nan.
