Saurari premier Radio
27.4 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKawuna sun rabu a majalisar dokokin Kano kan yadda za'a rage yawaitar...

Kawuna sun rabu a majalisar dokokin Kano kan yadda za’a rage yawaitar afkuwar kifewar kwale-kwale a jihar

Date:

Kamal Umar Kurna

An samu rabuwar kai a majalisar dokokin jihar Kano bayan da dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Madobi, Sulaiman Mukhat Ishaq, ya gabatar da kudurin da ya bukaci gwamnatin Kano ta samar da hanyar da za’a rage yawaitar afkuwar kifewar kwale-kwale a fadin jihar tare da taimaka wa wadanda suka gamu da ibtila’in.

Da yake gabatar da kudirin dan majalisar ya ce akwai bukatar daukar matakan gaggawa a gwamnatance domin kawo karshen yadda kifewar kwale-kwale ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi a kananan hukumomin dake wajen kwaryar birnin Kano, musamman yadda a makon da ya gabata aka samu mutuwar fiye da mutum 10 a kogin dake tsakanin karamar hukumar Madobi da Kura.

Mukhtar ya ce la’akari da yadda al’ummar kananan hukumomin Madobi, Kura da Garun Malam suka dogara da kogin wajen gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum, akwai bukatar gwamnatin Kano ta samar musu da kwale-kwale na zamani sabanin na gargajiya da suke amfani da shi a yanzu.

Da yake nuna goyon baya kan kudirin, dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dambatta, Murtala Musa Kore, ya ce akwai bukatar majalisar da gwamnatin Kano su dinga gaggautawa wajen taimakawa wadanda suka gamu da ibtila’in kifewar kwale-kwale duba da yadda kusan wata daya kenan da ya gabatar, aka gabatar da makamancin kudurin a gaban majalisar domin a taimakawa wadanda suka gamu da kifewar kwale-kwalen a karamar hukumarsa ta Dambatta amma har yanzu babu abinda aka yi ddomin duk wadanda abin ya shafa suna cikin matsanancin hali.

Sai dai da yake mayar da martani ga dan majalisar na Dambatta, shugaban masu rinjaye kuma dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dala, Lawan Husaini ya kalubalanci takwaransa na Dambatta, inda yace kalamansa sun ci karo da yadda ake gudanar aiki a majalisa da kuma gwamnati.

Bayan muharar, majalisar ta amince da korafin na dan majalisar karamar hukumar Madobi tare da dage zaman ta ya zuwa gobe Talata.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...