Saurari premier Radio
27.4 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiMUTUM AƘALLA 22 NE SUKA MUTU BAYAN DA MOTAR SAFA DA SUKE...

MUTUM AƘALLA 22 NE SUKA MUTU BAYAN DA MOTAR SAFA DA SUKE CIKI TA AFKA WANI RAMI A AREWACIN PAKISTAN

Date:

Mutum aƙalla 22 ne suka mutu bayan da motar safa da suke ciki ta afka wani rami a arewacin Pakistan

Jami’ai sun ce haɗarin ya faru ne a kusa da garin Azad Pattan, da ke kan iyakar lardin Punjab da Kashmir ta ƙarƙashin mulkin Pakistan.

A wani haɗarin na daban kuma aƙalla masu ziyarar ibada 12 ne suka mutu a kan hanyarsu ta komawa gida, a babbar hanyar Makran, da ke kudu maso yammacin ƙasar ta Pakistan.

Alamu sun nuna cewa direban motar da mutanen ke ciki ya kasa sarrafa motar ne, bayan da birkinta ya shanye.

Dukkanin haɗurran biyu na yau Lahadi sun faru ne bayan da a Ć´an kwanakin da suka gabata wasu masu ziyarar ibada ‘yan Pakistan ɗin su 28 suka mutu a wani haɗarin motar safa a Iran.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...