Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta samar da sabbin matakan kariya domin hana shigar da sakamakon zaɓe marasa inganci ko waɗanda ke nuna ƙuri’un da suka zarce adadin masu kaɗa ƙuri’a a shafinta na IReV.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan ne yayin wani taro a Chatham House da ke birnin London, inda ya ce matakan na daga cikin shirye-shiryen tabbatar da sahihancin babban zaɓen 2027.
Amupitan ya ce binciken da hukumar ta gudanar bayan zaɓen 2023 ya nuna cewa manyan matsalolin tattara sakamakon zaɓe sun fi faruwa a cibiyoyin haɗa sakamako.
Ya ƙara da cewa hukumar ta inganta na’urorin BVAS tare da samar da ƙarin na’urori domin rage matsalolin da aka fuskanta a zaɓukan baya.
Hukumar ta kuma tsara gudanar da gwajin na’urorin tantance masu zaɓe da tura sakamako a faɗin Najeriya ranar 28 ga Nuwamba, 2026.
