Saurari premier Radio
22.6 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiGwamnatin jihar Kebbi ta bai wa ma'aikatan kiwon lafiya na wucen gadi...

Gwamnatin jihar Kebbi ta bai wa ma’aikatan kiwon lafiya na wucen gadi fiye da takardu 200 na kama aiki dindindin.

Date:

Gwamntin jihar Kebbi ta bai wa ma’aikatan kiwon lafiya na wucin gadi su fiye da 200 takardun kama aiki na dindindin bayan wani korafi da suka yi a lokacin gabatar da shirin ‘A Faɗa A Cika’ na BBC Hausa da haɗin gwiwar Gidauniyar MacArthur.

Haka ma gwamnatin ta bayyana cewa ta cika alkawarin sama wa manoman shinkafa da suka yi korafi fanfunan ban ruwa har kimanin 6,000.

Gwamnan jihar Dakta Nasir Kauran Gwandu da ya ke amsa tambaya a lokacin shirin da ya gudana a jihar Kebbi ya ce tattaunawar da aka yi ta haifar da alfanu.

Ba iya jihar Kebbi ba, kusan a jihohin wannan kasa akwai ma’aikatan lafiya na wucin gadi da dama dake ci gaba da aikin taimakon marasa lafiya, duk kuwa da yadda ake fama da karancin likitoci a wannan kasa, lamarin da ya sanya wasu gwamnonin kan mayar da hankali wajen tabbatar da takardar daukar aiki ga ma;aikatan wucin gadin a lokaci zuwa lokaci.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...