Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin ci gaba da tsare wani mutum mai suna Muhammad Ibrahim, wanda ake zargi da aikata laifukan ta’addanci da safarar alburusai, a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa ranar 16 ga Nuwamba, 2026, lokacin da za a fara sauraron shari’arsa.
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ce ta gurfanar da Muhammad Ibrahim a gaban kotun, bisa tuhume-tuhume guda huɗu da suka haɗa da ta’addanci, mallaka da safarar alburusai ba bisa ƙa’ida ba, ɓoye bayanan safarar makamai da kuma damfara ta hanyar amfani da takardun shaida na bogi.
Ana zargin wanda ake ƙarar da safarar alburusai masu rai guda 170 na bindigar AK-47, waɗanda ya ɓoye a cikin wani kwandon sanyaya kaya domin kai wa wani mutum mai suna Imrana Halilu a ƙauyen Dankama da ke Jihar Katsina, a watan Fabrairun 2025.
Haka kuma, DSS ta zarge shi da taimaka wa ƙungiyoyin ta’addanci ta hanyar jigilar alburusai da ake zargin za a yi amfani da su wajen ayyukan ta’addanci.
A tuhuma ta huɗu kuma, hukumar ta bayyana cewa Muhammad Ibrahim ɗan ƙasar Nijar ne, inda ake zarginsa da samun lambar shaidar zama ɗan ƙasar Najeriya (NIN) ta hanyar yaudara.
Ana zargin cewa waɗannan laifuka sun saɓa wa tanade-tanaden dokar hana ta’addanci ta shekarar 2022 da kuma dokar laifukan intanet ta shekarar 2015.
