Yara biyar ’yan gida ɗaya sun rasu, yayin da wasu uku suka jikkata, sakamakon wani hatsarin mota da ya faru a Jihar Gombe.
Hatsarin ya faru ne a safiyar Talata, 27 ga Oktoban 2026, a mahadar Kanadi Academy, kusa da dandalin APC, lokacin da wata motar ɗaukar ruwa ta yi karo da babur mai ƙafa uku da ke ɗauke da yaran zuwa makaranta.
Hukumar kiyaye afkuwar haɗurra ta kasa, FRSC, ta tabbatar da mutuwar mutane huɗu, ciki har da yara biyu, a wani hatsarin mota da ya haɗa babur mai kafa uku da tankar ruwa a jihar Gombe.
Hukumar ta kuma bayyana cewa wasu mutane biyu sun samu raunuka a hatsarin.
Sai dai ba’a bayar da ƙarin bayani kan musabbabin hatsarin ko halin da waɗanda suka jikkata suke ciki ba.
