Hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta kama wasu mutane 5, wadanda suka hadar da Alhaji Muhammed Kabara babban sakatare a ma’aikatar kananan hukumomi da kula da harkokin masarautu, biyo bayan zarginsu da sama da fadi da wasu makudan kudade da sunan kwangilar magunguna.
Mai magana da yawun hukumar Kabiru Kabiru ya tabbatarwa da manema labarai kama mutanen, yana mai cewa a binciken da suka fara sun gano cewa kananan hukumomi 44 na ware wasu kudade da suna kwangilar magani kuma kudin na fita amma babu maganin a kasa.
Daga cikin mutanen da hukumar ta kama akwai shugaban karamar hukumar Tarauni Alhaji Abdullahi Bashir, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar shugabannin kanannan hukumomi ta kasa reshen nan Kano, sai kuma shugaban kamfanin magunguna na Novomed Garba Kwankwaso, dan’uwan madugun darikar kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, biyo bayan yadda zargin ya karkata kansa a badakalar.
Wadanda aka kama din anan zarginsu da sama da fadi da makudan kudade wadanda ake zargin sun taskace su da sunan baiwa kamfanin na NOVOMED kwangilar magunguna raba magunguna ga kananan hukumomi 38, duk kuwa da cewa hakan ya sabawa dokokin gudanar da ayyukan gwamnati.
Mai magana da yawun hukumar ya kara da cewa wadanda suka kama din yanzu haka suna tsare a maajiyar hukumar, ya yin da hukumar ta ci gaba da gudanar da bincike kan badakalar.