Shugaban Jami’ar Al-Istiqama da ke Sumaila, Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, ya ce kafa jami’ar a yankin ya kasance wani shiri na musamman da aka tsara domin kawo karshen ƙalubalen rashin samun manyan makarantun ilimi a yankunan karkara.
Sanata Kawu ya bayyana hakan ne yayin bikin haɗin gwiwar yaye ɗaliban jami’ar na shekarun karatu 2023 zuwa 2025, inda ɗalibai dubu ɗaya da ɗari da huɗu suka kammala karatunsu.
Kawu ya ce rashin samun damar karatun manyan makarantu a yankunan karkara na tilastawa matasa ƙaura zuwa birane domin neman ilimi da sauran damammaki, lamarin da ke ƙarawa birane cunkoso da matsin lamba kan abubuwan more rayuwa.
A nasa jawabin, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana farin cikinsa da kafuwar jami’ar, yana mai cewa manufofinta sun yi daidai da shirin gwamnatinsa na bunƙasa ilimi.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamnan na cewa gwamnatinsa ta biya kuɗin ci gaba da karatun ɗalibai 85 da ke karatun likitanci da injiniya, tare da tunatar da cewa ya ayyana dokar ta-baci kan harkar ilimi tun bayan hawansa mulki.
