Saurari premier Radio
25.8 C
Kano
Sunday, September 22, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiNIMET ta ce za a kwashe kwanaki uku nan gaba ana sheka...

NIMET ta ce za a kwashe kwanaki uku nan gaba ana sheka ruwa a Kano ba kakkautawa.

Date:

Hukumar kula da yanayi ta kasa NiMet, ta yi gargaɗin samun ambaliya a a nan jihar Kano da mama wasu jihohin ƙasar nan sakamakon mamakon ruwan sama da za a samu kwanan nan.

Hukumar ta ce jihohin da suka haÉ—a da Kano, da Katsina, da Zamfara, da Jigawa da Kebbi da Kaduna, da kuma jihar Adamawa na cikin barazanar fuskantar ambaliyar ruwa, don haka ne ta yi kira ga mahukuntan jihohin su É—auki matakan kare al’ummominsu.

Tuni dai dama ambaliyar ta fara É“arna a wasu jihohin Najeriya inda aka samu asarar rayuka da ta dukiyoyi.

Alhaji Bashir Idris Garga, darakta a hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriyar NEMA ya ce wannan ruwan saman da za ayi na kwana uku ba ƙaƙautawa zai sanya magudanar ruwa da dama ba a cika damuwa da yashe su ba su cike wanda daga bisani ruwan zai malala har ya je yayi ɓarna.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...