Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da kalaman shugaban Amurka Donald Trump da ke ayyana ƙasar a matsayin mai take haƙkin gudanar da addini, bayan zargin kisan ɗimbin mabiya adddinin Kirista.
Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar a safiyar yau Asabar ɗauke da sa hannun kakakinta Kimiebi Ebienfa ta ce kalaman na Trump basu bayyana ainahin halin da Najeriyar ke ciki ba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, mabanbantan addinai na rayuwa a waje guda tare da yin aiki tare ba tare da kowanne ɓangare ya cutar da wani ba, tsawon shekaru ba tare da rikici ba.
- Nijeriya ta yi asarar naira biliyan 118 a cikin watanni biyu – NOSDRA
- Shugaba Tinubu ya gana da sabbin hafsoshin tsaro na kasa
Sanarwar ta ruwaito gwamnatin na yabawa da kulawar ƙasashen duniya kan halin da Najeriyar ke ciki a lamurran da suka shafi kare haƙƙin ɗan adam da ƴancin gudanar da addinai amma wannan zargi babu ƙanshin gaskiya a ciki.
Tun farko a jiya Juma’a ne shugaba Donald Trump na Amurka cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social ya ayyana Najeriyar a matsayin ƙasar da ke take haƙƙin gudanar da addini, kalaman da ke zuwa bayan fitar wasu zargi daga ɗan majalisar Amurkan a baya-bayan nan da ke cewa ana yiwa mabiya addinin kirista kisan ƙare dangi a cikin.
