
Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar Kula da Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Kano (SUBEB), tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Ƙasa (UBEC), sun ƙaddamar da gasar wasannin motsa jiki ta ɗaliban makarantun ilimin bai ɗaya ta shekarar 2026, wato BESS 2026.
An buɗe gasar ne a filin wasa na Jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, inda Shugaban SUBEB Kano, Malam Yusuf Kabir, ya ce manufar gasar ita ce bunƙasa wasanni a makarantu da kuma gano ɗaliban da ke da hazaka domin wakiltar jihar Kano a gasa daban-daban.
Shugaban hukumar, wanda Daraktan Kula da Harkokin Makarantu, Malam Ibrahim Yahuza, ya wakilta, ya ce ana shirya gasar ne duk shekara domin ƙarfafa sha’awar wasanni tsakanin ɗalibai.
A nasa jawabin, Malam Ibrahim Yahuza ya bayyana cewa ɗalibai daga ƙananan hukumomi 44 na jihar za su fafata a cibiyoyi takwas, da suka haɗa da Wudil, Rano, Dawakin Kudu, Danbatta, Gwale, Tudun Wada, Gwarzo da Bichi.
Ya ce wasannin da za a fafata sun haɗa da tsallen igiya, tseren gudu, tsallake shinge da jefa ƙwallo daga tsugunne.
A sakamakon gasar ranar farko a cibiyar Wudil, ƙaramar hukumar Wudil ce ta zo ta farko da maki 15, sai Albasu da maki 13, yayin da Ajingi ta zo ta uku da maki 9.
Hukumar ta kuma bayyana cewa za a ci gaba da gasar a cibiyar Rano a ranar Alhamis.
