Aƙalla mutum 41 aka kashe, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon hare-haren da aka kai wa jama’a daban-daban a Jihar Filato cikin mako guda da ya gabata.
Yankunan da aka kai wa hari sun haɗa da Bassa, Riyom, Bokkos da Ƙaramar Hukumar Mangu.
Hakazalika, an ruwaito cewa ɗaruruwan mutane sun rasa matsugunansu, an kuma ƙone gidaje da ba a san adadinsu ba.
Ɗaya daga cikin mafi munin hare-haren ya auku ne a ranar 8 ga watan Yuni, a ƙauyen Bauda da ke yankin Langai a Ƙaramar Hukumar Mangu.
’Yan bindiga sun shiga garin da sassafe, inda suka kashe mutum bakwai tare da ƙona gidaje 61, ciki har da cocin COCIN LCC.
A daren ranar, wasu ’yan bindiga sun sake kai hari garin Chinchim da ke yankin Mangu, inda suka kashe mutum takwas.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Mangu, Emmanuel Bala, ya tabbatar da aukuwar hare-haren.
