Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta bayyana cewa jami’anta sun kashe ’yan bindiga 18 tare da kuɓutar da mutane 45 da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Bakori ta Jihar Katsina.
A cewar hukumar, an gudanar da samamen ne tsakanin Satumba da Oktoban 2026, bisa bayanan sirri da haɗin gwiwar wasu hukumomin tsaro da Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro.
DSS ta kuma ce ta kama wasu da ake zargi da safarar makamai a jihohin Filato, Nasarawa, Kaduna da Benue, tare da tarwatsa hanyoyin samar da makamai da ake dangantawa da ƙungiyar ESN a Kudu maso Gabashin Najeriya.
Hukumar ta ƙara da cewa ta kashe wani kwamandan ƙungiyar ISWAP, Abdussamad Ohida, a Jihar Ondo.
DSS ta jaddada aniyarta ta ci gaba da kai farmaki kan hanyoyin samar da makamai da sauran kayayyakin da masu aikata laifuka ke amfani da su.
