Mutum aĆalla 22 ne suka mutu bayan da motar safa da suke ciki ta afka wani rami a arewacin Pakistan
Jami’ai sun ce haÉarin ya faru ne a kusa da garin Azad Pattan, da ke kan iyakar lardin Punjab da Kashmir ta ĆarĆashin mulkin Pakistan.
A wani haÉarin na daban kuma aĆalla masu ziyarar ibada 12 ne suka mutu a kan hanyarsu ta komawa gida, a babbar hanyar Makran, da ke kudu maso yammacin Ćasar ta Pakistan.
Alamu sun nuna cewa direban motar da mutanen ke ciki ya kasa sarrafa motar ne, bayan da birkinta ya shanye.
Dukkanin haÉurran biyu na yau Lahadi sun faru ne bayan da a Ć´an kwanakin da suka gabata wasu masu ziyarar ibada ‘yan Pakistan Éin su 28 suka mutu a wani haÉarin motar safa a Iran.