Ƙungiyar, mai suna Kaduna State Muslim-Christian Network for Good Governance, ta ce kalaman ministan sun yi daidai da abin da wasu mazauna jihar suka fuskanta a lokacin mulkin El-Rufai daga shekarar 2015 zuwa 2023
A cikin wata sanarwa da shugabanta Tahir Tanko da sakatarenta Steven Kefas suka sanya wa hannu, ƙungiyar ta zargi tsohuwar gwamnatin da wasu manufofi da ayyuka da take cewa sun ƙara rarrabuwar kawuna a jihar
Ƙungiyar ta ambaci korar ma’aikata da yawa, rushe wasu kasuwanni da gidaje, batun sarakunan gargajiya da kuma yadda aka tafiyar da matsalar tsaro a lokacin gwamnatin a matsayin wasu daga cikin abubuwan da take da korafi a kansu
Ta kuma yi kira ga masu sukar Ministan Tsaro da su gabatar da hujjoji maimakon mayar da batun zuwa rikicin ƙabilanci ko addini
Wannan na zuwa ne bayan da Janar Christopher Musa ya yi kakkausar suka ga tsohuwar gwamnatin El-Rufai a wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya zarge ta da rarraba al’ummar Kaduna da kuma wasu manufofin da ya ce sun shafi tsaro da zaman lafiyar jihar
