Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya jaddada cewa ba zai janye daga takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba, duk da hukuncin kotun da ya soke tsare-tsaren shugabancin jam’iyyar ADC.
Atiku ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a, inda ya ce babu wata barazana ko matakin shari’a da zai sa ya yi watsi da burinsa na siyasa.
Ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ƙoƙarin raunana jam’iyyun adawa, yana mai cewa ba za su amince da yunƙurin mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya ba.
Atiku ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su kasance masu haƙuri da haɗin kai, tare da ci gaba da shirye-shiryen yaƙin neman zaɓe.
A halin yanzu, jam’iyyar ADC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya soke shugabancin David Mark da matakan da shugabancin ya ɗauka, ciki har da zaɓen Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.
