Saurari premier Radio
24 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaMinistan Gidaje ya nuna damuwa kan yadda aikin gina Gidaje 500 ke...

Ministan Gidaje ya nuna damuwa kan yadda aikin gina Gidaje 500 ke tafiya a Kano

Date:

Ministan Gidaje da ci gaban birane, Ahmed Musa Dangiwa, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda aikin gina gidaje 500 ke tafiya a nan jihar Kano.

Ahmad Dangiwa ya bayyana rashin jin dadinsa ne a lokacin da ya kai ziyarar duba yadda aikin ke gudana a karshen mako.

Ya kuma ce matuka aikin ba ya sauri kamar yadda aka tsara tun da fari zai gudana.

Ma’aikatar Gidaje da ci gaban birane ta kasa ce dai ta fara gina gidaje 500 a Jihar Kano, a wani yunkuri na gina sabbin muhali ga masu bukata.

Aikin ginin gidajen wanda aka yi wa lakabi da Renewed Hope Estate na gudana ne wani a kauye dake Lambu a karamar hukumar Tofa a arewacin Kano.

Aikin ya haÉ—a da gina gida mai É—aki biyu, É—aki É—aya, da kuma waÉ—anda ke da É—aki uku.

Ya gargadi wadanda aka bai wa aikin gina gidajen da ya hanzarta ko kuma gwamnati ta kwace aikin daga hannusa.

Sai dai wanda aka bai wa kwantiragin aikin wanda manajan kamfanin Haruna Lawal ya wakilta, ya gayawa ministan tabbacin za su kara himma don ganin aikin ya kammala kafin cikar wa’adin da aka debar musu.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...